Ikechukwu Uche ya tsawaita kwantiraginsa

Image caption A kakar wasanni na bana ya zura kwallaye hudu a ragar abokan karawarsu

Dan wasan gaba na Nigeria, Ikechukwu Uche ya rattaba hannu a kwantiragin shekara biyu da tsawaita zamansa a Villarreal.

Dan wasan kasa da kasan mai shekaru 30 a koma kulob din na Spaniya ne a watan Agusta na shekarar 2011, kuma a yanzu zai kai 2017 kenan tare da kulob din.

"Ina matukar farin cikin tsawaita kwantiragin da na yi da kulob din" Ikechukwu ya gaya wa BBC.

Dan wasan ya koma kulob din Villarreal ne daga kulob din Zaragoza kuma daga bisani aka bada aronsa ga Granada.

Ikechukwun ya koma Villarreal lokacin da aka mayar da kulob din kasan teburin premier a 2012/13 kuma ya zama dan wasan da ya fi kowa zura kwallo, inda ya zuba kwallaye 14 a raga, abin da ya maido kulob din saman teburi.