U- 17: An raba jaddawalin kofin nahiyar Afirka

CAF U-17 Afirka Hakkin mallakar hoto
Image caption Kasashe hudu ne za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya da Chile za ta karbi bakunci a badi

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF, ta raba jaddawalin wasannin cin kofin matasa 'yan kasa da shekaru 17 na Afirka da Niger za ta karbi bakunci a badi.

CAF ta raba jaddawalin gasar cin kofin matasan ne a ranar Lahadi a Cairo, wanda za a fara tsakanin 15 ga watan Fabrairu zuwa 1 ga watan Maris 2015.

Rukunin farko ya kunshi mai masaukin baki Niger da Nigeria da Guinea da Zambiya da za suyi wasanninsu a filin General Seyni Kountche a Niamey.

Rukuni na biyu yana dauke da mai rike da kofin Ivory Coast da Afirka ta Kudu da Mali da kuma Kamaru da za su kara a filin wasa na Municipal dake Niamey.

Dukkan kasashen da suka kai wasan daf da na karshe za su wakilci Afirka a gasar cin kofin duniya na matasa 'yan kasa da shekaru 17 da Chile za ta karbi bakunci badi.