Liverpool da Arsenal sun tashi wasa 2-2

Liverpool Team Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Liverpool tana mataki na 10 a teburin Premier

Liverpool da Arsenal sun tashi wasa 2-2 a gasar Premier wasan mako na 17 da suka fafata ranar Lahadi a filin wasa na Anfield.

Liverpool ce ta fara zura kwallo a ragar Arsenal ta hannun Coutinho, kuma nan da nan Arsenal ta farke kwallonta ta hannun Debuchy daf da za a tafi hutu.

Bayan da aka dawo ne daga hutu Arsenal ta kara kwalo na biyu ta hannun Giroud a minti na 19 da dawo wa, kuma Liverpool ta farke ta hannun Skrtel.

Liverpool ta karasa karawar da yan wasa 10 a fili, bayan da aka bai wa Fabio Borini jan kati sakamakon ketar da ya yi wa Santi Cazorla.

Kungiyoyin sun raba maki a tsakaninsu, kuma Arsenal tana matsayi na shida da maki 27 a teburin Premier, yayin da Liverpool ta koma mataki na 10 da maki 21.