An raba jadawalin kofin zakarun Afirka

CAF Champion League Hakkin mallakar hoto
Image caption Za a fara wasannin Champion League da Confederation Cup a badi

Hukumar kwallon kafar Afirka CAF ta raba jadawalin gasar cin kofin zakarun Afirka na Champion League da Confederation Cup na badi.

Jadawalin da CAF ta fitar a taron da ta gudanar a a Alkahira, ya kunshi kungiyoyi 58 da za su fafata a cin kofin Champion League da kuma 56 da za su kara a Confederation Cup.

Za a fara da wasannin share fage daga ranar 13 da 14 da kuma 15 ga watan Fabrairu, sai karawa na biyu daga 27 da 28 ga watan Fabrairu da 1 ga watan Maris din badi.

A gasar cin kofin zakarun Afirka kulob din ES Setif da Coton Sport da AC Leopards da Al Ahly da TP Mazembe da CSS da EST ba za su buga wasan share fage ba.

Kuniyoyin da ba za su buga wasan share fage a gasar Confederation Cup kuwa sun hada da Asec Mimoas da Zamalek da Djoliba da AS Vita da Orlando Pirates da Ahli Shendi da Club Africain da kuma ESS.