Ingila za ta ci gaba da kara kaimi a wasanni

Roy Hodgson Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ingila ce ta daya a rukuni na biyar, inda ta lashe wasanni hudu da ta buga

Kocin tawagar kwallon Ingila, Roy Hodgson, ya ce za su ci gaba da kara kaimi, duk da haskakawar da suke yi a wasannin neman tikitin shiga gasar cin kofin nahiyar Turai.

Ingila, wadda ke matsayi na daya a rukuni na biyar, ta lashe dukkan wasannin hudu da ta buga na neman gurbin shiga gasar da za a buga a shekarar 2016.

Nasarar da tawagar ta Ingila ta samu ta zo ne bayan da ta kasa taka rawar gani a gasar kofin duniya da aka yi a Brazil, inda ta kasa kai wa wasan zagaye na biyu.

Hodgson ya ce suna samun ci gaba a wasanninsu, kuma suna yin aiki tukuru tare da 'yan wasa musamman wajen da suke da rauni.