Carrick ne zakaran kwallon kafa - Ferguson

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Ferguson ya ce Carrick ne zakaran kwallon Turai

Tsohon kociyan Manchester United Sir Alex Ferguson ya ce Michael Carrick ne zakaran wasan kwallon kafar Turai.

Kulob din dai ya lashe wasanni shida cikin bakwai tun da Carrick -- mai shekaru 33 -- ya dawo buga wasa bayan raunin da ya ji a idon sahu.

Ferguson ya ce, "Ina ganin Michael ne zakaran dan wasan tsakiya a Turai. Ina ganin shi ne dan wasan da ya fi kwarewa a wasannin."

Ya kara da cewa yana alfaharin ganin United ta hau matsayi na uku a gasar Premier tun da Van Gaal ya karbi ragamar gudanar da kungiyar.

A ranar Juma'a aka ayyana Carrick a matsayin mataimakin kyaftin na kulob din.