Senegal da Guinea za su yi atisaye a Morocco

Afircan Cup of Nation Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Za a fara gasar cin kofin Afirka daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun badi

Kasashen Senegal da Guinea za su yi atisayen tunkarar gasar cin kofin nahiyar Afirka na badi da Equitorial Guinea za ta karbi bakunci a Morocco.

Guinea wadda ta buga wasannin neman tikitin shiga gasar a Morocco sakamakon kaucewa kamuwa da cutar Ebola, za ta yi atisayen ne a Casablanca.

Ita kuwa Teranga Lions wadda za ta bayyana sunayen 'yan wasan da za su wakilce ta a gasar, za ta yi nata atisayen ne a garin El Jadida.

Kuma kasashen biyu za su buga wasan sada zumunta a tsakaninsu ranar 13 ga watan Janairu.

Haka kuma Senegal za ta kara da gabon, yayin da Guinea za ta fafata da matasan Morocco 'yan shekaru 23 duk dai a wasannin sada zumuntar