Louis van Gaal ya gode wa Ferguson

Louis van Gaal Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United tana mataki na uku a teburin Premier

Kocin Manchester United Louis van Gaal, ya ce amincewa da kwarin gwiwar da yake samu a wajen Sir Alex Freguson ne ya sa aikin sa ya ke da sauki a United.

A kakar wasan farko da van Gaal ya ke horar da United ya kai ta mataki na uku a teburin Premier duk da 'yan wasanta da dama na yin jinya.

Van Gaal, mai shekaru 63, ya ce ya ji dadi da amanar da aka bashi a United, kuma dalilin da ya sa ya ke gudanar da aikinsa a natse.

Sau 40 'yan kwallon United na yin jinya tun lokacin da van Gaal ya karbi ragamar jagorantar kulob din.

United din za ta buga gasar Premier da Newcastle ranar Juma'a ba tare da Daley Blind da Marcos Rojo da Luke Shaw da Marouane Fellaini da kuma Ander Herrera da suke yin jinya.