Arsene Wenger ya yabi Charlie Austins

Charlie Austin Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Dan wasan yana haskakawa a gasar Premier bana

Kocin Arsenal ya yabi dan wasan QPR, Charlie Austin, da cewa dan kwallo ne mai hazaka da kwarewa a shirye-shiryen da suke na fafatawa a kofin Premier ranar Juma'a

Austin, mai shekaru 25, ya zura kwallaye 11 a gasar Premier, har da kwallaye ukun da ya ci West Bromwich a karawar da QPR ta doke su ranar Asabar.

Dan wasan ya koma QPR ne daga Burnley a farkon kakar bara, kuma saura watanni 18 kwantiraginsa ya kare da kulob din.

Wenger ya ce dan kwallon ya kware wajen zura kwallo a raga, sannan yana damun masu tsaron baya a wasa.

Kocin Queens Park Rangers, Harry Redknapp, ya ce ba zai bari wani kulob ya dauke masa dan wasansa ba a watan Janairu.