Chelsea za ta iya lashe kofuna hudu - Matic

Image caption Nemanja Matic

Dan kwallon Chelsea, Nemanja Matic ya ce kungiyarsa za ta iya lashe kofuna hudu a kakar wasa ta bana.

Matic ya ce Chelsea ta na damar yin abinda ba a taba yi ba a Ingila na lashe kofuna hudu wato na Premier da Champions da FA da kuma na League Cup.

Matic ya koma Chelsea ne daga Benfica a kan fan miliyan 21 a watan Junairu.

Ya ce "Ina tunanin muna da wannan damar. Zamu iya."

Dan kwallon na Serbia mai shekaru 26 ya ce " Ina da kwarin gwiwa a kan wannan tawagar, komai na iya faruwa."