Muntari da Boateng ba sa cikin tawagar Ghana

Image caption Ghana ta zargi 'yan wasa da rashin biyyaya

Sabon kocin Ghana, Avram Grant ya gayyaci 'yan wasa 31 wadanda daga cikinsu zai zabi wadanda za su wakilci kasar a gasar cin kofin Afrika na badi.

Sai dai bai gayyaci Sulley Muntari da Kevin-Prince Boateng ba wadanda aka dakatar lokacin gasar cin kofin duniya da ta wuce.

Tawagar:

Masu tsaron gida: Razak Braimah (Mirandes, Spain), Adams Stephen (Aduana Stars), Fatau Dauda (AshGold), Ernest Sowah (Don Bosco, DR Congo)

'Yan wasan baya: Harrison Afful (Esperance, Tunisia), John Boye (Erciyesspor, Turkey), Jonathan Mensah (Evian, France), Jeffery Schlupp (Leicester City, England), Awal Mohammed (Maritzburg, South Africa), Kwabena Adusei (Mpumalanga Black Aces, South Africa), Baba Rahman (Augsburg, Germany), Gyimah Edwin (Mpumalanga Black Aces, South Africa), Samuel Inkoom (Houston Dynamo, USA), Daniel Amartey, (FC Copenhagen, Denmark)

'Yan wasan tsakiya: Rabiu Mohammed (Krasnodar, Russia), Emmanuel Agyemang-Badu (Udinese, Italy), Afriyie Acquah (Parma, Italy), Solomon Asante (T.P. Mazembe, DR Congo), Christian Atsu (Everton, England), Mubarak Wakaso (Celtic, Scotland), Andre Ayew (Olympique Marseille, France), Alfred Duncan (Sampdoria, Italy), Albert Adomah (Middlesbrough, England), Frank Acheampong (Anderlecht, Belgium), Adu Kofi (Malmo, Sweden), Ibrahim Moro (AIK Stockholm, Sweden)

'Yan wasan gaba: Jordan Ayew (Lorient, France), Abdul-Majeed Waris (Trabzonspor, Turkey), Asamoah Gyan (Al Ain, UAE), Kwesi Appiah (Cambridge United, England) David Accam (Chicago Fire, USA)