Zola ya zama sabon kocin Cagliari

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Zola ya jagoranci West Ham na tsawon shekaru biyu

An nada Gianfranco Zola a matsayin kocin kungiyar Cagliari a Italiya.

Dan shekaru 48, ya maye gurbin Zdenek Zeman wanda kungiyar ta kora a farkon wannan makon.

Zola wanda tsohon kocin West Ham ne, ya yi ritaya a kwallo lokacin yana tare da Cagliari kuma ba ya jagorantar wata tawaga tun lokacin da ya bar Watford a watan Disambar 2013.

A baya ya murza leda tare da Chelsea na tsawon shekaru bakwai.

Wasanni biyu kacal Cagliari ta samu galaba a kakar wasa ta bana a Serie A.