An bukaci sa wasan kwamfuta a Olympics

Hakkin mallakar hoto CCP Games
Image caption Miliyoyin jama'a na sha'awar kallon wasan kwamfuta

Mutumin da ya kirkiro wasan bidiyo na kwamfuta na yaki (World of Warcraft), ya nemi da a sanya wasan, wanda aka fi sani da e-sports, a jerin wasannin da ake yi a gasar Olympics.

Rob Pardo, wanda har zuwa watan Yuli shi ne, shugaban kirkire-kirkire na kamfanin Blizzard Entertainment, ya ce wasa yanzu yana da fassara da yawa.

Ya ce wasannin bidiyo yanzu sun kai matsayin wasannin da ke jawo 'yan kallo da dama, kamar yadda ya sheda wa BBC.

Sai dai Mr Pardo, ya ce, wasan na bidiyo na fuskantar kalubale na samun karbuwa a wurin masu kallon wasanni na zahiri.

Masu wasan Chess ma sun dade suna neman a sanya wasan cikin jerin wasannin Olympics, amma hukumar Olympics din ba ta yarda ba.

Tana mai cewa wasa ne da ya shafi tunani da kwakwalwa, amma ba wasan motsa jiki ba, saboda haka ta ki yarda.

Hakkin mallakar hoto

Wasannin kwamfuta na kwararruka (e-sports), a yanzu sukan jawo 'yan kallo miliyoyi.

Mutane 40,000 ne suka shiga filin wasa domin kallon wani wasan karshe na kwamfuta, wanda aka yi a birnin Seoul, na Korea ta Kudu, a kwanakin nan.

Wasu mutanen kuma da dama suka kalli wasan ta intanet, wasu kuma a wuraren haduwar jama'a daban-daban a fadin duniya.