Zakaran kwallon Afrika: Enyeama na ciki

Hakkin mallakar hoto
Image caption sunan enyeama

Sunayen mai tsaron gida na Nigeria, Vincent Enyeama da dan wasan tsakiyar Ivory Coast, Yaya Toure da na Aubameyang dan asalin kasar Gabon ne a kan jerin sunayen da hukumar kwallon kafa ta Afrika, CAF ta fitar don fitar da wanda zai dauki kambun zakaran dan wasa na shekarar 2014.

Toure wanda ya ke bugawa kulob din Manchester City kwallo, ya karbi irin wannan kambun a shekaru ukun da suka gabata, abin da ya sanya shi zama dai-dai da Samuel Eto na Kamaru da Abedi Pele na Ghana.

Idan har ya sami nasara a karo na hudu, Toure zai zama dan wasa na farko da ya karbi kambun har sau hudu a jere.

Za a sanar da wanda ya samu nasarar daukar kambun a ranar takwas ga watan Janairu a birnin Legas da ke Najeriya.