Giroud ya yi nadamar yin gware

Olivier Giroud Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Giroud ba zai buga wasanni uku ba

Mai horar da 'yan wasan Arsenal, Arsene Wenger, ya ce ya cancanta a korar da aka wa Olivier Giroud daga wasa bayan da ya yi wa dan wasan QPR gware.

Sai dai Wenger ya ce Giroud ya yi nadamar abin da ya aikata.

An dai bai wa Giroud jan katin sallama bayan da ya yi wa dan wasan QPR Nedum Onuoha gware a wasan da Arsenal din ta yi nasara da ci 2-1.

"Lallai ya cancanci a ba shi jan katin amma amfani da kalmar hauka da wasu ke yi, ya yi tsauri da yawa."

Yanzu haka Giroud ba zai buga wasannin uku ba wadanda suka hada da karawarsu da West Ham da Southhampton da kuma wasansu da Stoke a gasar FA Cup.