Ana yi wa Chelsea makarkashiya- Mourinho

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Alkalin wasa Anthony Taylor ya ce Fabregas da gangan ya fadi

Jose Mourinho ya ce ana yi wa Chelsea makarkashiya bayan da alkalin wasa ya ki ba su fanareti lokacin da Fabregas ya fadi a haduwarsu da Targett na Southampton.

A ranar Lahadin nan aka yi wasanni tara na gasar kwallon kafar ta Premier, ta Ingila,na mako na 19, wadda Chelsea ke ci gaba da jagoranta.

Ga yadda wasannin suka kasance;

Tottenham 0 : 0 Man United ; Southampton 1 : 1 Chelsea ; Aston Villa 0 : 0 Sunderland.

Sai Hull City 0 : 1 Leicester City ; Manchester City 2 : 2 Burnley ; QPR 0 : 0 Crystal Palace.

Sannan Stoke City 2 : 0 West Bromwich ; West Ham United 1 : 2 Arsenal.

Sai kuma Newcastle United 3 : 2 Everton ;ranar Litinin Liverpool za ta kara da Swansea.

Chelsea ce ta daya a tebur da maki 46, sai Man City mai maki 43, wadda Man United ke bi mata baya da maki 36.

Southampton ce ta hudu da maki 33, yayin da Arsenal ta cira zuwa matsayi na biyar da maki 33 ita ma.

A can kasa kuma Crystal Palace na matsayi na 18 da maki 16, sai Burnley ita ma da maki 16, yayin da Leicester ke zaman ta karshe( ta 20) mai maki 13.