An tuhumi Cisse da yunkurin ta-da-zaune-tsaye

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Idan aka same shi da laifi, za a iya hana Cisse buga wasanni uku

Hukumar kwallon kafar Ingila, FA tana tuhumar dan wasan Newcastle United, Papiss Cisse da laifin yunkurin tayar-da-zaune-tsaye.

Kociyan Everton, Roberto Martinez, ya ce Cisse ya yi sa'a da ba a kore shi daga fili ba bayan ya doki dan wasansa Seamus Coleman da gwiwar hannu da gangan a fafatawar da Everton ta buge Newcastle 3-2.

A lokacin wasan ne dai Cisse ya zura kwallonsa ta biyar a cikin wasanni shida na gasar Premier da Newcastle ta buga, cikinsu kuma ta sha kashi sau hudu.

Yanzu dai an ba shi daga nan zuwa karfe shida na yamma a ranar Talata mai zuwa domin ya kare kansa game da tuhumar da ake yi masa.

Idan aka sami Cisse da laifi, za a iya hana shi buga wasanni uku.