West Brom ta kori kociyanta

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption West Brom ita ce ta 16 a gasar Premier

Kungiyar West Brom ta kori kociyanta Alan Irvine bayan sun sha kaye a wasanni bakwai cikin tara da suka yi a gasar Premier ta Ingila.

Kayen da suka rika sha ya sa kungiyar ta yi kasa sosai a tebirin gasar domin kuwa ita ce ta 16.

Irvine, mai shekaru 56, ya zama kociyan kungiyar ne a watan Yuni bayan sauke Pepe Mel, kuma an ba shi kwantaragin watanni 12 ne.

A ranar jajiberen sabuwar shekara ne West Brom za ta je gidan West Ham inda za su fafata, sai dai a wannan karon Rob Kelly ne zai jagorance ta tare da taimakon Keith Downing.