Wenger na so a hukunta masu faduwa da gangan

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger ya ce hukuncin ne kawai zai sa 'yan wasa su daina faduwa da gangan

Kociyan Arsenal Arsene Wenger yana so a kafa hukuma mai zaman kanta wacce za ta hukunta 'yan wasan da ke faduwa da gangan a filin kwallo.

Wannan batu na faduwar 'yan wasa da gangan dai ya yi suna domin kuwa ya shafi 'yan wasan Chelsea da dama.

Wenger, mai shekaru 65, ya ce ya kamata hukumar ta kunshi mutanen da suka kware a fagen kwallon kafa ta yadda za su yi "hukunci kan duk abin da ya nuna karara cewa faduwa aka yi da gangan".

Ya ce,"Ba wai ina yin adawa da faduwar da 'yan wasa ke yi da gangan ba ne, amma hukuncin ne kawai zai sa su daina yin hakan."