An dakatar da Cisse daga buga wasanni uku

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cisse ba zai buga fafatawar da za su yi da Burnley da Leicester da kuma Chelsea ba.

Hukumar kwallon Ingila ta dakatar da dan wasan Newcastle Papiss Cisse daga buga wasanni uku, bayan da aka same shi da yin keta da gangan.

Cisse ya doki dan wasan Everton, Seamus Coleman da gwiwar hannu a karawar da suka doke su 3-2 a gasar Premier.

Saboda haka Cisse ba zai buga fafatawar da za su yi da Burnley da Leicester da kuma Chelsea ba.

Cisse, mai shekaru 29, shi ne jagaba a dan wasan da ya fi zura kwallo a Newcastle, a inda ya zura kwallaye tara jumulla.