Pulis ne zai zama sabon kocin West Brom

Hakkin mallakar hoto All Sport
Image caption Ana tsammani Pulis ba zai fuskanci matsala ba

Za a nada Tony Pulis a matsayin sabon kociyan West Brom domin maye gurbin Alan Irvine, wanda aka kora daga aiki.

Pulis dai ya taba zama kociyan Stoke da Crystal Palace, kuma ana sa rai za a nada shi ne ranar Alhamis.

Kazalika, ana sa ran shi ne zai jagoranci kungiyar a fafatawar da za ta yi da West Ham.

Kodayake har yanzu babu cikakken bayani game da nadin nasa, amma ana gani ba zai fuskanci wata matsala ba.