An gabatar da Torres ga magoya bayan Atletico

Fernando Torrees Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption dan wasan zai buga karawar da za suyi da Real Madrid ranar Laraba a Copa del Rey

Kulob din Atletico Madrid ya gabatar da Fernando Torres a gaban magoya bayansa su 45,000 a filinsa na Vicente Calderon ranar Lahadi.

Shekaru bakwai da rabi ke nan da Torres, mai shekaru 30, ya bar Atletico, kulob din da ya fara taka leda tun yana yaro ya kuma koma Liverpool wasa.

Dan wasan ya koma Spaniya taka leda ne aro daga kulob din AC Milan na Italiya, wanda ya dauko shi daga Chelsea na Ingila.

Torres ya koma Chelsea wasa daga Liverpool a shekarar 2011 a matsayin dan kwallon da aka sayo mafi tsada a tarihi kan kudi fam miliyan 50.

Dan kwallon ya buga wa Atletico tamaula daga tsakanin 2001-2007, wanda ya zura kwallaye 84 a raga a wasanni 214 da ya buga.