Bouna ba zai buga wa Guinea kwallo ba

Bouna Sarr Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Dan kwallon ya amince ya mayar da hankalinsa wajen buga wa kulob dinsa

Kulob din Metz na Faransa ya sanar da cewa Bouna Sarr, ba zai buga wa Guinea gasar cin kofin nahiyar Afirka ta bana ba.

Kocin Guinea Michel Dussuyer ne ya saka sunan Sarr a cikin tawagar 'yan wasan da za su wakilci kasar a gasar, kwallon kafa mafi girma da za a gudanar a Afirka.

Sarr, wanda aka haifa a Faransa ya ki amsa goron gayyatar Guinea ne domin ya mayar da hankali wajen buga wa Metz tamaula.

Kasar Guinea tana rukuni na hudu wanda ake gani shi ne mafi zafi da ya kunshi Kamaru da Ivory Coast da kuma Mali.

Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ne daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun bana a Equatorial Guinea.