'Babu wanda ya kori Gerrard daga Liverpool'

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kyaftin din Liverpool da zai koma taka leda a Amurka

Tsohon dan kwallon Liverpool, John Barnes, ya ce bai yi tsammani idan da wanda ya tilastawa Steven Gerrard ya bar kulob din ba.

Gerrard, mai shekaru 34, zai bar Anfield a karshen kakar wasan bana lokacin ne kwantiraginsa zai kare, kuma ya yanke hakan ne saboda ba a saka shi a wasa sosai.

Jamie Carragher tsohon dan wasan Liverpool wanda ya buga kwallo tare da Gerrard ya ce ya kamata kulob din ya hana dan wasan barin Anfield.

Barnes ya kara da cewa Gerrard yana sha'awar buga wasanni sosai kuma rashin buga wasannin ne yasa dan kwallon ya yanke shawarar barin Liverpool.

Gerrard ya ce zai koma buga wasa a kasar Amurka idan kwantiraginsa ya kare da Liverpool a bana, amma bai bayyana kulob din da zai koma ba.