Carver na kwadayin samun kocin Newcastle na dindindin

John Carver Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption wasanni biyu aka bai wa Carver kafin a dauko sabon mai horar da 'yan wasa

Kocin rikon kwaryar kulob din Newcastle, John Carver, ya ce yana da sha'awar horar da kulob din a matsayin kocin dindindin.

An bai wa Carver, mai shekaru 49, kocin rikon kwaryar Newcastle lokacin da kulob din ya amince wa Alan Pardew ya tattauna da Crystal Palace lokacin da suke bukatar daukar sa.

Bayan da Crystal Palace ta sanar da daukar Pardew a matsayin sabon kocinta ne, Carver ya nuna kwadayin a ba shi ragamar horar da Newcastle na dindindin.

Wannan ce kaka ta biyu da Carver ke tare da kulob din, wanda ya yi aiki tare da Sir Bobby Robson, sai dai ya ce har yanzu bai sanar wa da shugaba Mike Ashley bukatar sa ba.

Kocin Derby County Steve McClaren da na Hull City Steve Bruce sun karyata rade-radin da ake yi cewar an yi musu tayin aikin kocin kulob din.