Valencia ta doke Real Madrid da ci 2-1

valencia Madrid
Image caption Sai da AC Milan ta doke Real Madrid a wasan karshe na shekarar 2014 da suka fafata a Dubai

Valencia ta doke Real Madrid da ci 2-1 a gasar La Liga wasan mako na 17 da suka kara ranar Lahadi.

Doke Madrid da aka yi an taka mata burkin nasara a wasanni 22 a jere ba tare da an doke ta ba.

Cristiano Ronaldo ne ya fara zura kwallo a bugun fenariti, kuma kwallonsa na 33 da ya ci a kakar wasan bana.

Valencia ta farke kwallonta a minti na bakwai da dawo wa daga hutu ta hannun Antonio Barragan, kafin Otamendi ya kara zura kwallo na biyu a raga.