Rafael da Shaw sun ji rauni a kofin FA

Louis van Gaal Hakkin mallakar hoto
Image caption Louis van Gaal ya ce wasan an sa jiki sosai an kuma yi gogayya

'Yan kwallon Manchester United Rafael da Shaw sun ji rauni lokacin da suke buga Gasar Kofin Kalubale da suka kara da Yeovil ranar Lahadi.

Rafael ya ji rauni ne a mukamukinsa, yayin da Shaw ya kasa karasa wasan sakamakon jin ciwo da ya yi a kafarsa.

Cikin 'yan wasan United da suke yin jinya sun hada da Ashley Young da kuma Antonio Valencia.

Ander Herrera da Angel Di Maria ne suka ciwa United kwallaye da suka doke Yeovil da ci 2-0 a gasar kofin kalubalen.

Rabon da United ta dauki Kofin Kalubale tun lokacin da ta doke Millwall a shekarar 2004.