Senegal za ta auna girman raunin Mane da Sakho

Sadio Mane Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Senegal na kokarin kaucewa zuwa gasar da 'yan wasa masu rauni

Kasar Senegal za ta auna raunin da Sadio Mane da Diafra Sakho suke jinya domin tantance idan za su iya buga mata gasar cin kofin Nahiyar Afirka.

Mane mai taka leda a Southampton yana fama da rauni a gwiwarsa, har ma koci Ronald Koeman ya ce dan wasan ba zai iya buga gasar cin kofin Afirka ba.

Shi kuwa Sakho wanda yake buga wa West Ham kwallo yana fama ne da ciwon baya da yakan hana shi gudu sosai.

Kocin Senegal Alain Giresse ya ce 'yan kwallon biyu za su hadu da tawagar 'yan wasan kasar a Morocco domin auna girman raunukan nasu.