Ana tuhumar Berahino da tuki a cikin maye

Saido Berahino Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ana rade-radin cewa dan kwallon zai iya barin West Brom a bana

'Yan sanda na tuhumar dan wasan West Bromwich Albion kuma dan wasan gaba na Ingila, Saido Berahino da laifin tuki bayan ya sha barasa.

An kama dan kwallon ne, mai shekaru 21, da misalin karfe 4 na yamma a ranar 22 ga watan Oktoba.

A ranar 19 ga watan Janairu ne dan kwallon zai gurfana a gaban kotun arewacin Cheshire a Runcorn domin amsa tuhumar da ake yi masa

Berahino dan wasan tawagar kwallon Ingila ya zura kwallaye 13 daga cikin wasannin 24 da ya buga wa West Brom a kakar wasan bana.