Equatorial Guinea ta nada Becker kocinta

afcon 2015 Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka daga 17 ga watan Janairu zuwa 8 ga watan Fabrairun bana

Kasar Equatorial Guinea ta nada Esteban Becker a matsayin sabon kociyan tawagar kwallon kafarta domin maye gurbin Andoni Goikoetxea.

Becker, mai shekaru 50, dan kasar Amurka shi ne ya horar da tawagar kwallon kafar kasar ta mata da ya jagoranta zuwa gasar cin kofin Afirka a shekarar 2012.

Kuma kocin ne zai shirya 'yan wasan da za su wakilci kasar a gasar cin kofin nahiyar Afirka nan da kwanaki 11 da za su fara karawa da Congo ranar 17 ga watan Janairu.

Equatorial Guinea ta ki sabunta kwantiraginta da Goikoetxea, inda ta ce ya karya yarjejeniyar da suka kulla a inda yaki halartar atisayen da kasar ta yi a Portugal ranar 16 ga watan December.

Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar 17 ga watan Janairu, wanda Equatorial Guinea take rukuni daya da Congo da Burkina Faso da Gabon.