FIFA: Yarima Ali zai kalubalanci Blatter

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Ali Bin Al Hussein ya ce ya kamata a samu sauyi

Mataimakin shugaban Fifa, Yarima Ali Bin Al Hussein na Jordan zai fafata da Sepp Blatter a takarar shugabancin hukumar.

Yarima Ali , mai shekaru 39, zai tsaya takara ne a zaben wanda za a yi a ranar 29 ga watan Mayu, a yayin da Blatter, mai shekaru 78, zai nemi a zabe shi domin yin wa'adi na biyar a jere.

Yarima Ali said: "Lokaci ya yi da ya kamata a samu sauyi daga irin rikice rikicen da wannan hukuma da kuma harkawar wasanni ke ciki."

Ya kara da cewa abokan aikinsa na cikin mutanen da suka karfafa masa giwa domin yin takarar.