Bony yana tattaunawa da Manchester City

Wilfred Bony Hakkin mallakar hoto huw evans picture agency
Image caption Bony ya zura kwallaye 20 a gasar Premier a kalandar shekarar 2014

Manchester City tana tattaunawa da dan wasan Swansea City, Wilfred Bony domin ya koma buga mata kwallo a watan Janairun nan.

Ana hangen dan wasan, dan kasar Ivory Coast, zai kai farashin fam miliyan 30, idan har City tana son ya dawo kulob dinta da taka leda.

Tun a baya kociyan Swansea, Garry Monk ya ce sai an taya Bony a farashi mai tsoka kafin su sayar da shi ga duk kulob din da yake son daukar dan wasan.

Bony ya koma Swansea daga Vitesse Arnhem a shekarar 2013 a matsayin dan kwallon da kulob din ya saya mafi tsada kan kudi fam miliyan 12.

Dan kwallon zai wakilci kasarsa a gasar cin kofin nahiyar Afirka, saboda haka ana sa ran kammala cinikinsa bayan rufe gasar kwallon kafa mafi girma a Afirka.