Manchester United ta dauki Victor Valdes

Victor Valdes Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United tana matsayi na uku a teburin Premier Ingila

Tsohon golan Barcelona, Victor Valdes, ya amince da tayin da Manchester United ta yi masa na ya koma buga mata kwallon kafa.

Dan kasar Spaniya, wanda ya yi atisaye da United domin murmurewa daga raunin da ya ji a gwiwarsa, ya amince da kwantiragin watanni 18.

Valdes, mai shekaru 32, wanda kwantiraginsa da Barcelona ya kare, ya dauki kofunan La Liga shida da na Zakarun Turai uku da kulob din.

Daukar Valdes da United ta yi zai sa mai tsaron gararta mai jiran kar-ta-kwana Anders Lindegaard zai iya barin kulob din.

Haka kuma ana tunanin makomar gola David De Gea, mai shekaru 24, wanda kwantiraginsa da United zai kare a shekarar 2016.