Messi ya fi kowanne dan kwallo daraja

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Akwai hamayya mai zafi tsakanin Messi da Ronaldo

An bayyana dan kwallon Barcelona Lionel Messi a matsayin wanda ya fi kowanne dan kwallo a duniya daraja inda aka kimanta shi a kan Euro miliyan 220.

Wannan kimar ta sa ya shiga gaban babban abokin hammayarsa, Cristiano Ronaldo na Real Madrid wanda darajarsa ta kai Euro miliyan 133.

Hakan nan kuma an bayyana dan kwallon Chelsea, Eden Hazard a matsayin mafi daraja a gasar Premier ta Ingila inda darajarsa ta kai Euro miliyan 99.

Mujallar Inside Spainish Football wacce ta wallafa wannan kididdiga ta ce tawagar Real Madrid ce ta fi kowacce yawan 'yan wasa masu tsada.

Jadawalin 'yan wasa 10 mafi daraja:

  • Lionel Messi (Barcelona) : Euro miliyan 220
  • Cristiano Ronaldo (Real Madrid) : Euro miliyan 133
  • Eden Hazard (Chelsea) : Euro miliyan 99 million
  • Diego Costa (Chelsea) : Euro miliyan 84 million
  • Paul Pogba (Juventus) : Euro miliyan 72 million
  • Sergio Agüero (Manchester City) : Euro miliyan 65 million
  • Raheem Sterling (Liverpool) : Euro miliyan 63 million
  • Francesc Fàbregas (Chelsea) : Euro miliyan 62 million
  • Alexis Sánchez (Arsenal) : Euro miliyan 61 million
  • Gareth Bale (Real Madrid) : Euro miliyan 60 million

Bayanai:Mujallar Inside Spainish Football