Ana tuhumar Mourinho da rashin da'a

Jose Mourinho
Image caption Chelsea ce ke matsayi na daya a teburin Premier

Hukumar kwallon kafar Ingila tana tuhumar kocin Chelsea, Jose Mourinho, da rashin da'a sakamakon jawabin da ya yi bayan da suka tashi wasa da Southampton.

Mourinho ya yi ikirari cewar ana kokarin murkushe kulob dinsa, bayan da suka tashi kunnen doki a filin St Mary ranar 28 ga watan Disamba.

Ya kuma yi wannan ikirarin ne sakamakon kin ba su fenariti da ya yi zargi an yi a lokacin da aka yi wa Cesc Fabregas keta.

Sai dai kuma daga baya ya nemi afuwar saboda kalaman da ya yi dangane da kwarewar alkalin wasa Kevin Friend.

Hukumar ta bai wa Mourinho nan da 13 ga watan Janairu domin ya kare kansa daga tuhumar da take yi masa.