Manchester United ta kammala daukar Valdes

Victor Valdes Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Valdes ya yi atisaye da United bayan ya bar Barcelona

Manchester United ta kammala daukar tsohon golan Barcelona, Victor Valdes, a matsayin mai tsaron ragarta mai jiran kar-ta-kwana.

Koci Louis van Gaal ne ya sanar da daukar dan wasan, wanda ya rattaba kwantiragin watanni 18 da yarjejeniyar za a iya tsawaita ta tsawon shekara daya.

Dan kasar Spaniya, ya yi atisaye da United domin murmurewa daga raunin da ya ji a gwiwarsa, bayan da ya bar Barcelona.

Valdes, mai shekaru 32, ya dauki kofunan La Liga shida a Barcelona da na Zakarun Turai uku da kulob din.

Daukar Valdes da United ta yi zai sa mai tsaron ragarta mai jiran kar-ta-kwana Anders Lindegaard zai iya barin kulob din.