Senegal za ta hana Sakho buga wa West Ham

Diafra Sakho Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption West Ham ce ta sanar da cewa Sakho ba zai iya buga gasar kofin Afirkar ba

Kasar Senegal za ta yi kokarin hana Diafra Sakho buga wa West Ham tamaula zuwa tsawon makonni uku da za a buga gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Mahukuntan Senegal sun tuhumi West Ham da hana dan wasan ya wakilci kasarsa a gasar cin kofin Afirkan.

Senegal ta bukaci ta auna girman raunin ciwon bayan da West Ham ta ce dan wasan mai shekaru 25 yana fama da shi.

Shugaban kwallon kafar Senegal Augustin Senghor ya ce za su shigar da korafinsu ga hukumar kwallon kafar Ingila da kuma ta FIFA.

Senegal tana rukuni na uku da ya kunshi Ghana da Afirka da Kudu da Algeria, wanda za su fafata a filin wasa na Malabo da ke Equatorial Guinea.