Galaxy ba za ta bayar da aron Gerrard ba

Steven Gerrard Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Gerrard zai koma Galaxy bayan karshen kakar wasan bana

Shugaban Los Angeles Galaxy, Chris Klein, ya ce ba wata maganar bayar da aron Steven Gerrard ga wani kulob din da zarar ya dawo buga musu wasa.

Gerrard, mai shekaru 34, tsohon dan kwallon Ingila zai koma taka leda Amurka ne a karshen kakar wasan bana, bayan shafe shekaru 25 a Liverpool

Frank Lambert, mai shekaru 36, ya koma kulob din New York City daga Chelsea, amma suka bayar da shi aro ga Manchester City.

Gerrard shi ne kyaftin din Ingila na biyu da zai koma Los Angeles Galaxy taka leda, bayan David Beckham da ya je kulob din a shekarar 2007.