Neil ya zama kociyan Norwich

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption Neil ya ce a shirye yake ya fuskanci kalubale

Norwich City ya nada dan wasan Hamilton Academical, Alex Neil, a matsayin sabon kociyan kulob din.

Neil, mai shekaru 33, ya maye gurbin Neil Adams wanda ya sauka daga mukaminsa ranar Litinin bayan ya kwashe watanni tara yana jan ragamar kulob din.

Neil dai ya bar kulob din Hamilton a matsayi na uku a gasar Premier ta Scotland, bayan ya kai su ga samun ci gaba a kakar wasannin ta badi.

Neil ya ce, "Na ji dadi sosai da na zama kociyan kulob mai matsayi irin Norwich. A shiye nake na fuskanci kalubale".