Chelsea ta kawar da Man City a saman tebur

Chelsea Hakkin mallakar hoto EPA
Image caption Yanzu Chelsea na da maki 49

Klub din Chelsea ya karbe saman teburin gasar Premier bayan da Manchester City ta tashi da ci 1-1 da Everton.

Dan wasan Man City Fernandinho ne ya zira kwallon City a cikin minti na 74 kana dan wasan Everton Naismith ya farke kwallon a cikin minti na 78.

Yanzu haka Chelsea ta baiwa Man City tazarar maki biyu bayan da suka lallasa Newcastle.

Hakan na nufin Chelsea na da maki 49 yayin da Manchester City ke da maki 47.