Afirka ta kudu ta maye gurbin Phungwayo

Ayanda Gcaba Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Za a fara gasar cin kofin nahiyar Afirka ranar 17 ga watan Janairu

Tawagar kwallon kafar Afirka ta Kudu ta maye gubin Partrick Phungwayo da Ayanda Gcaba a cikin 'yan wasan da za su wakilce ta a gasar cin kofin nahiyar Afirka.

Hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu ta ce likitoci za su duba lafiyar Gcaba da takardunsa na tafiye-tafiye kafin ya halarci sansanin 'yan wasa a Gabon ranar Talata.

Tun a ranar Asabar Phungwayo mai tsaron baya ya koma Afirka ta Kudu domin a duba raunin da ya ji a gwiwarsa.

Kociyan Afirka ta Kudu Ephraim Shakes Mashaba, ya ce ya yi bakin ciki da Phungwayo ya ji rauni, amma ya yi murna da aka maye gurbinsa da Gcaba.