Southampton ta koma matsayi na 3 a Premier

United Southampton Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Soutampton ta dare mataki na uku a teburin Premier

Manchester United ta yi rashin nasara a hannun Southampton da ci daya mai ban haushi a gasar Premier da suka fafata a Old Trafford.

Dusan Tadic ne ya zura kwallo a raga, bayan da ya samu dama daga tamaular da Graziano Pelle ya buga ta doki turke.

Wannan ce nasarar farko da Southampton ta doke United a Old Trafford a gasar Premier a shekaru 27 baya.

Southampton ta koma mataki na uku a teburin Premier da maki 39, a inda United ta fado matsayi na hudu da maki 37.