Cristiano ne gwarzon dan kwallon duniya

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Cristiano ya kara zama dan kwallon duniya

Dan wasan gaba na kulob din Real Madrid, Cristiano Ronaldo ya sake zama gwarzon dan kwallon kafa na duniya na 2014.

Kaftin din Portugal wanda ya lashe kyautar karo na biyu a jere, ya doke dan wasan Barcelona, Lionel Messi da mai tsaron gida na Bayern Munich, Manuel Neuer.

'Yar wasan Wolfsburg da Germany, Nadine Kessler ita ce ta zamo ta daya a fannin kwallon kafa na mata ta duniya, a inda James Rodrigues ya lashe kyautar zura kwallaye mafi yawa a shekarar 2014.

Koci Joachim Low na Germany wadda ta dauki kofin kwallon kafa na duniya a 2014, ne ya dauki kambun kocin da ya fi kowanne a 2014.