Za a sanar da wanda ya lashe Ballon d'Or

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Messi ya lashe gasar sau hudu, Ronaldo kuma sau biyu. Neuer bai taba lashe gasar ba

A ranar Litinin ne Hukumar Kwallon kafa ta duniya, FIFA za ta bayyana wanda ya lashe gasar gwarzon dan wasan kwallon kafa na shekarar 2014.

Dan wasan Real Madrid, Cristiano Ronaldo da na Barcelona, Lionel Messi da kuma na Bayern Munich Manuel Neuer na cikin masu yin takarar lashe gasar.

Messi ya lashe gasar sau hudu, yayin da Cristiano Ronaldo ya lashe sau biyu. Neuer bai taba lashe gasar ba.

A shekarar ta 2014 ne dai Messi ya kafa tarihin zama dan wasan da ya fi yawan kwallaye a gasar La Liga da gasar Uefa.

Takwaran Messi a Barcelona, Ivan Rakitic da kuma zakaran tseren motoci na duniya Marc Marquez sun ce Messi ne ya kamata ya sake lashe gasar.