City ta bai wa Schalke aron Nastasic

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Mancini ne ya sayo Nastasic daga Fiorentina

Kulob din Manchester City ya bai wa Schalke aron dan wasansa Matija Nastasic zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Tsohon kociyan City, Roberto Mancini ne ya sayo dan wasan -- mai shekaru 21-- daga Fiorentina a watan Agustan shekarar 2012.

Sai dai bai tabuka abin kirki ba a wasan farko da ya buga a karkashin jagorancin, Manuel Pellegrini, kuma bai taka leda a kakar wasa ta bana ba.

Wasan karshe da ya buga wa kulob din shi ne wanda suk doke Arsenal 3-0 a gasar Community Shield a watan Agusta.