Cristiano Ronaldo ya yafe wa Bale

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Cristiano da Gareth Bale a filin wasa

Gwarzon dan kwallon duniya, Cristiano Ronaldo ya roki masoya kulob din Madrid da su yi wa Gareth Bale uzuri bayan da ya shimfidi kwallo zuwa kan mai-uwa-dawabi maimakon ya mika wa Cristiano kwallon su yi taba-in-taba.

Bale, wanda ya samu damar zura kwallo a wasan da kulob din nasa ya lallasa Espanyol da ci 3 da nema amma ya bata wa Cristiano rai, duk da cewa daga bisani ya yi masa uzuri.

Ya ce abin da Gareth ya yi ranar Asabar ba wani laifi ba ne saboda hakan zai iya faruwa da kowa, "nima ya na faruwa da ni".

Cristiano ya kuma ja hankalin masoya Real Madrid da su ci gaba da karfafa masa gwiwa saboda kasancewarsa dan wasa mai muhimmanci ga kulob din.