Oussama zai bar Liverpool zuwa Al-Ahli

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Oussama Assaidi zai koma Al-Ahli

Dan wasan Liverpool, Oussama Assaidi, zai koma kulob din Al-Ahli na Dubai.

Oussama, mai shekaru 26, dan asalin Morocco ya kwashe tsawon kakar Gasar Premier ta bara a Stoke, inda ya zura kwallaye biyar kafin daga bisani ya koma Liverpool.

Sai dai kuma kokarin komawar da dan wasan yake yi zuwa Al-Ahli ta Dubai ya kawo karshen zaman nasa a kulob din na Birtaniya.

Dan wasan zai je kulob din na Al-Ahli a kan yarjejeniyar shekaru uku da rabi.

Assaid ya taka rawar gani a Stoke yayin gasar Premier a watan Disamba na 2013, a lokacin da kulob din ya samu nasara kan Chelsea da ci uku da biyu.