Watson ta doke Sloane karo biyu a jere

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Heather Watson 'yar wasan tennis

'yar wasan kwallon tennis 'yar birtaniyar nan, Heather Watson ta doke takwararta ta Amurka Sloane Stephens karo biyu a jere a kokarin neman samun fafatawa a wasan dab-da-na-kusa da na karshe da za a buga a birnin Hobart na Australia, ranar 19 ga watan Janairu.

Watson mai shekaru 22 ta doke Sloane din ne bayan ta lallasa ta da ci shida da uku a karon farko, sannan ta kara mata da ci shida da daya, a karo na biyu, dukkaninsu a cikin mintina 64.

Wannan nasarar ta ba wa Watson damar zuwa wasan dab-da-na-kusa da na karshe a inda za ta kara da 'yar wasan tennis ta kasar Italiya, Roberto Vinci.

Heather Watson ta ce "na shirya tsaf don fuskantar wasan".