Crystal Palace ya karbi aron Sanogo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wenger ya ce Sanogo dan wasa ne da ke da himma

Crystal Palace ya karbi aron dan wasan Arsenal, Yaya Sanogo zuwa karshen kakar wasa ta bana.

Dan wasan -- mai shekaru 21-- shi ne dan wasa na farko da kociya, Alan Pardew, ya karbo aro tun lokacin da ya dawo kulob din daga Newcastle a watan nan na Janairu.

An yi hasashen cewa Sanogo zai koma Bordeaux na Faransa sai dai kociyan Arsenal, Arsene Wenger ya fi so ya ba da aronsa ga kulob din Ingila.

Pardew ya ce "Dan wasan matashi ne da zai taka muhimmiyar rawa a tamaula nan gaba."