Sampdoria ta tuntubi Everton kan Eto'o

Samuel Eto'o Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon dan kwallon Real Mallorca da Barcelona da Inter Milan da Anzhi Makhachkala da Chelsea

Kila Samuel Eto'o zai iya barin Everton, bayan Sampdoria ta tuntubi kulob din Ingila idan zai sayar mata da dan wasan.

Tsohon dan kwallon Kamarun, ya koma Everton ne daga kulob din Chelsea a watan Agusta kan yarjejeniyar kwantiragin shekaru biyu.

Haka kuma dan kwallon ya zura kwallaye uku daga cikin wasannin 14 da ya buga wa Everton a kakar wasan bana.

Idan har Eto'o ya bar Everton zai zamo dan kwallo na biyu da zai bar kulob din bayan da Hallam Hope ya koma Bury.

Tuni kociyan Everton, Roberto Martinez, ya tabbatar da cewa kungiyoyin kwallon kafa na tuntubarsu kan batun idan za a sayar musu da Eto'o.